Sakacin gwamnati ne zai sa a cigaba da kisan mutane a Filato—Gwamnan Kaduna

0
26
Uba Sani

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana kudurinta na ganin cewa an bi haƙƙin ƴan asalin jihar da aka kashe a jihar Filato yayin wani hari da ya auku a ranar Asabar.

A cewar gwamnatin jihar, mutum 12 daga cikin ƴan jihar Kaduna ne aka kashe a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato, a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, cikin wata mota mallakin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Harin ya jikkata mutum 16, kuma dukkansu na kwance a asibiti, daga cikin mutane 31 da ke cikin motar a lokacin.

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana alhininsa kan lamarin, inda ya ce ya yi magana da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, yana mai jaddada cewa ba za su yarda rayukan waɗanda suka mutu su salwanta a banza ba.

“Na kira gwamnan Filato na nuna masa matuƙar ɓacin ranmu kan wannan mummunan lamari. Mun yarda da zaman lafiya, amma ba za mu lamunci irin wannan hali ba,” in ji Gwamna Uba Sani.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ya tattauna da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, da kuma mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, dangane da wannan hari.

Ya ce ana buƙatar gaggauta ɗaukar mataki domin kawo ƙarshen kashe-kashen da ke faruwa a jihar Filato.

Sai dai Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa takwaransa na jihar Filato ya shaida masa cewa tuni aka kama mutum 22 da ake zargi da hannu a harin.

Duk da haka, Gwamnan Kaduna ya ce akwai buƙatar faɗaɗa bincike domin gano sauran da suka da hannu a lamarin, tare da tabbatar da an hukunta su bisa doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here