Majalisar dattawa zata yi nazari akan ƙirƙiro sabbin jihohi 31

0
26

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima ya bayyana cewa zai yi nazari kan shawarwari 31 da ke neman ƙirƙirar sabbin jihohi a fadin ƙasar nan.

Kwamitin, wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ke jagoranta, ya bayyana cewa za a gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin jama’a na yankuna daban-daban a ranakun 4 da 5 ga watan Yuli, 2025.

Za a gudanar da zaman sauraron ra’ayoyin ne a lokaci guda a jihohin Legas (kudu maso yamma), Enugu (kudu maso gabas), Ikot Ekpene (kudu maso kudu), Jos (tsakiya), Maiduguri (arewa maso gabas), da Kano (arewa maso yamma).

A cikin wata sanarwa da mai bai wa mataimakin shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce kwamitin ya himmatu wajen tattara ra’ayoyin ‘yan Najeriya kan muhimman sauye-sauyen kundin tsarin mulki.

Mudashir ya bayyana cewa kwamitin ya karɓi buƙatu biyar na neman ƙirƙirar sabbin jihohi daga yankunan kudu maso yamma, kudu maso kudu, da arewa ta tsakiya, buƙatu bakwai daga arewa maso gabas, shida daga arewa maso yamma; da kuma uku daga kudu maso gabas.

Ya ƙara da cewa kwamitin zai kuma duba batutuwa masu muhimmanci na ƙasa kamar wandaa suka shafi ‘yancin kan ƙananan hukumomi, sauye-sauyen bangaren shari’a da na zaɓe, ‘yan sandan jihohi, da kuma shugabanci na haɗin gwiwa.

A cewarsa, daya daga cikin kudurorin na neman sanya ƙananan hukumomi a matsayin wani bangare na gwamnati da kundin tsarin mulki zai kare musu wa’adin aiki.

Wani kuduri na daban kuma yana neman kafa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa da za ta kula da zaɓukan ƙananan hukumomi, wato Hukumar Zaɓen Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NALGEC),” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here