Hare haren bata gari sunyi sanadiyar mutuwar mutane 30 a Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 30 sakamakon hare-haren da suka auku a kananan hukumomin Zuru da Danko-Wasagu.
Shugabannin kananan hukumomin biyu, Muhammad Gajere na Zuru da Hussaini Bena na Danko-Wasagu, ne suka bayyana hakan yayin da mataimakin gwamnan jihar, Umar Tafida, ya kai ziyarar jaje ga al’ummomin da abin ya shafa.
A cewar shugabannin, mutane 16 ne suka rasa rayukansu a Tadurga da ke karamar hukumar Zuru, yayin da wasu 14 suka mutu a kauyukan Kyebu da Yar-Kuka a yankin Waje na karamar hukumar Danko-Wasagu.
Sun kuma bayyana cewa ‘yan ta’addan sun sace dabbobi da wasu kayan masarufi masu daraja daga hannun al’umma.
Yayin ziyarar, Malam Umar Tafida, wanda ya wakilci gwamna Nasir Idris, ya miƙa sakon ta’aziyyar gwamnati ga al’ummar da abin ya shafa.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar na cikin alhini tare da dangin wadanda suka rasa rayukansu da kuma daukacin al’ummar masarautar Zuru.
Haka kuma, ya tabbatar wa da al’ummar yankin cewa gwamnati za ta dauki matakan ƙara tsaro, tare da rufe dukkan hanyoyin shigowa garuruwan Tadurga da Kyebu domin hana sake faruwar irin wannan hari a nan gaba.