Wani dalibi mai karatu a aji 3 a sashen koyar da kimiyyar sinadarai, a Fakutin Ilimi na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja, Abdulwahab Abubakar, ya rasa ransa bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi da makami ne suka kai masa.
Harin da ya faru a safiyar Litinin ya tayar da hatsaniya tsakanin daliban jami’ar, inda suka toshe manyan titunan Lapai-Agaie da Lapai-Minna, tare da yin zanga-zangar rashin ɗaukar matakan tsaro daga mahukuntan jami’ar da sauran hukumomi.
Wasu daga cikin daliban sun bayyana cewa hare-haren ‘yan fashin daji kan dalibai sun zamo ruwan dare a cikin watanni shida da suka gabata, amma ba a ɗauki mataki mai ƙarfi ba.
Majiyar Daily Trust ta bayyana cewa daliban da suka fusata sun lalata ofishin tsaron jami’ar, sannan wasu daga cikinsu sun mamaye fadar Sarkin Lapai domin bayyana ƙorafinsu.
Wani ɗalibi mai suna Mohammed Hassan ya ce makamancin wannan hari ya faru makon da ya gabata, inda wasu mata dalibai suka fuskanci fyade daga ‘yan fashin da suka yi wa ɗakunan kwana su dirar mikiya dauke da bindigu da sauran makamai, suna wawure kayayyakin daliban.
Rahotanni sun nuna cewa kisan na Abdulwahab ya faru da misalin ƙarfe 2 na safiyar Litinin a wani ɗakin kwanan ɗalibai da ke unguwar Ndakitabu, kusa da ƙofar shiga jami’ar da ke kan hanyar Lapai-Minna.
An bayyana cewa marigayin ya dawo makarantar da yammacin ranar Lahadi domin cigaba da karatu kafin a kai masa hari da safiyar Litinin.
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Hukumar gudanarwar jami’ar dai har yanzu ba ta fitar da wata sanarwa dangane da wannan sabon lamari ba, sai dai a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 12 ga Yuni, 2025, ta musanta faruwar hare-haren baya da fyaden da ake zargin sun faru.