Wasu da ba a san ko su waye ba sun sace Mai Shari’a E.G. Umokoro na babbar kotun Jihar Bayelsa, a garin Yenagoa, babban birnin jihar.
Mai Shari’a Umokoro, wanda ke jagorantar babbar kotu ta Bakwai a jihar, an ce an yi garkuwa da shi ne da misalin ƙarfe 7:30 na dare a ranar Asabar, a gaban wani shahararren gidan cin abinci da ke yankin Ekeki.
Motar da ya ke ciki a lokacin, wato baƙar mota kirar Toyota Prado, an bar ta a wurin bayan an yi garkuwa da shi.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, an ga yadda Mai Shari’ar ke ƙoƙarin ƙwacewa daga hannun masu garkuwar yayin da suke jan sa don tafiya dashi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Musa Muhammad, ya bayyana cewa rundunar ta tura jami’ai domin bin sahun masu laifin da kuma cafke su.