Gwamnatin Saudiyya ta bayyana “matuƙar damuwa” kan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin ƙera makaman nukiliya a Iran, tana mai jaddada buƙatar ƙasashen duniya su ƙara ƙoƙari wajen neman mafita ta siyasa a rikicin da ke kara tsananta tsakanin ƙasashen biyu.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar a daren jiya, ƙasar ta bayyana cewa wannan mataki na Amurka na iya haifar da mummunan tasiri ga zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki ɗaya.
“Saudiyya na kira ga dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin da su nuna hikima da haƙuri, tare da bin hanyoyin diflomasiyya domin kawo ƙarshen rikicin cikin lumana,” in ji sanarwar.
Harin da Amurka ta kai ya biyo bayan zargin da ta yi wa Iran da ci gaba da ƙera makaman nukiliya da kuma take dokokin ƙasa da ƙasa na hana yaɗa makamashi mai haɗari. Sai dai Iran ta musanta zargin, tana mai cewa shirinta na nukiliya na nufin amfani da makamashi ne cikin lumana.