Harin Amurka akan Iran ya saɓawa ka’ida—Burtaniya

0
28

Jakadan Iran a Birtaniya, Seyed Ali Mousavi, ya bayyana cewa harin da Amurka ta kai kan Iran ya saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Da yake zantawa da BBC, jakadan ya ce harin ya take ikon Iran a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yanci, yana mai cewa hakan ya saba wa ƙa’idodin hulɗar ƙasashe.

Sai dai, Mousavi ya ƙi bayyana cikakken bayani game da irin barnar da harin ya haifar ga cibiyoyin nukiliyar Iran, duk da tambayoyin da BBC tayi masa.

Wakiliyar BBC ta tambaye shi ko Iran za ta iya daina shirin ta na nukiliya da kuma kawo ƙarshen rikicin ta da Isra’ila, idan har Amurka ta sake kai mata farmaki.

A martaninsa, Mousavi ya ce kafin Isra’ila ta kai hari ga Iran, akwai tattaunawa da ke gudana tsakanin Iran da Amurka kan shirin nukiliyar ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here