Hare hare sunyi sanadiyar mutuwar ƴan Najeriya 59 a kwanaki biyu

0
53

Aƙalla mutane 59 ne suka mutu a hare-hare daban-daban guda huɗu da suka faru a jihohin Borno, Kano, Kebbi da Filato a ranakun Juma’a da Asabar.

A jihar Kebbi, mutane 30 ne suka rasa rayukansu a wani harin ƴan bindiga. A jihar Filato kuma, an kashe mutum 12 masu zuwa ɗaurin aure 

A jihar Borno kuwa, wata mata ta kai harin kunar bakin wake a wata kasuwar kifi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 12.

 A Kano, kuwa wani bam ɗin sojoji ne ya fashe a gefen hanya akan titin Eastern Bypass, a ranar Asabar, inda mutane biyar suka mutu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here