Amurka ta gargaɗi Iran kan daukar matakin ramuwar harin data kai mata

0
39
Donald Trump
Donald Trump

Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi gargaɗi ga gwamnatin Iran da ta guji mayar da martani kan harin da Amurka ta kai mata, yana mai jaddada cewa burin Shugaba Donald Trump shi ne ganin an samu zaman lafiya.

A cewar Hegseth, shugaba Trump ya bayyana a fili cewa ba ya son janyo tashin hankali ko barna, saboda abin da yake nema shi ne zaman lafiya, don haka ya kamata Iran ta bi wannan hanya ta lumana.

Ya ƙara da cewa Iran ba ta da wani riba a cikin mayar da martani, kuma hakan na iya kara dagula lamarin.

A sanyin safiyar Lahadi ne Amurka ta kaddamar da hare haren jirage marasa matuƙi akan tashoshin nukiliyar Iran guda uku, amma Iran tace babu asarar rai a harin, kuma hakan bai lalata kayan aikin nukiliyar ta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here