Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa dakataccen gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, da kuma gwamnan Bayelsa, Douye Diri, na dab da sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani biki na tarbar Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, zuwa jam’iyyar APC.
An gudanar da bikin ne a filin wasan na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, tare da wasu gwamnoni da sanatoci sun halarci bikin.
A ranar 6 ga Yuni, Gwamna Eno ya sanar da sauya sheƙarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Akpabio ya ce wannan sauyin sheƙa ba kawai ficewa daga wata jam’iyya ba ce, sai dai wani motsi ne da ke nuna haɗin kai.