Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta sanar da fara bincike kan waɗanda ake zargin sun lalata tutar yaƙin neman zaɓe ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka kafa a wani ɓangare na birnin Kano.
Wani bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna wasu matasa na yaga tutar tutar dake ɗauke da hoton Shugaba Tinubu, da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibril,.
Wannan bidiyon ya haifar da cece kuce a tsakanin ƴan siyasa, lamarin da ya sa rundunar ‘yan sanda ta fitar da gargaɗi mai ƙarfi kan aikata irin wannan ɓarna da tayar da hankali.
A cikin wata sanarwa da mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Hussaini Abdullahi, ya fitar, rundunar ta bayyana wannan aiki a matsayin laifi kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro.
Ya ce tuni rundunar ta fara bincike domin gano wadanda ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su gaban shari’a.
Rundunar ta bayyana cewa duk wani mai aikata nau’in lalata dukiyar jama’a ko gwamnati zai fuskanci hukunci mai tsanani, domin kuwa babu sassauci wajen aiwatar da doka akan kowa.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci jama’ar jihar da su zauna lafiya tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo hargitsi a cikin al’umma. Ya kuma tabbatar da jajircewar rundunar wajen tabbatar da doka da oda a fadin jihar.