Wata mace ta tayar da Bam a Borno, tare da kashe masu siyan abinci su 24

0
28

Wata mace ta tayar da Bam a Borno, tare da kashe masu siyan abinci su 24

Wata mata da ta kai harin kunar bakin wake ta kashe akalla mutane 24 tare da jikkata wasu da dama a wani mashahurin wurin cin abinci da ke garin Konduga, Jihar Borno mai nisan kimanin kilomita 36 daga birnin Maiduguri.

Lamarin ya faru ne da misalin Æ™arfe 10 na dare a ranar Juma’a, lokacin da matar ta tada wani abu mai Æ™arfi da ta É—aura a jikinta a cikin cunkoson jama’a da ake siyar da abinci.

Majiyoyin ‘yan sanda da suka tattauna da masanin tsaro, Zagazola Makama, sun tabbatar da cewa fashewar ta yi sanadin mutuwar mutane 24 maza da mata yayin da wasu da dama suka samu raunuka masu tsanani da matsakaici. Bom din ya tarwatse gaba ɗaya, sai kanta kawai aka samu a wurin da harin ya auku.

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji, ƙwararrun sashen EOD-CBRN na ‘yan sanda (masu cire abubuwan fashewa da suka haɗa da sinadarai, kwayoyin cuta, da makamashi masu illa), ƙungiyoyin dabarun aiki, ‘yan sa-kai na CJTF da maharba sun hanzarta zuwa wurin. An kuma rufe yankin gaba ɗaya, sannan ana gudanar da bincike mai zurfi, amma ba a samu wasu karin abubuwan fashewa ba.

Wadanda suka jikkata an garzaya da su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) domin kulawar gaggawa, yayin da gawarwakin wadanda suka mutu ma aka ajiye su a dakin ajiye gawa na asibitin. 

Hukumomi sun bayyana cewa ana ci gaba da tantance bayanan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata, tare da shirin mika gawarwakin ga iyalansu domin a binne su bisa tsarin addininsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here