Matasa sun kashe masu zuwa ɗaurin aure a jihar Filato

0
25

Aƙalla fasinjoji bakwai ne suka rasa rayukansu a daren Juma’a bayan da wasu matasa da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari kan wata motar haya mai ɗaukar mutane 18 a ƙaramar hukumar Mangu, Jihar Filato.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:47 na dare, a ranar 20 ga Yuni, 2025, kamar yadda rahoton kwararren mai sharhi akan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana. Motar dai na ɗauke da fasinjoji 28 daga wata jiha makwabciya zuwa ƙaramar hukumar Qua’an-Pan da ke Jihar Filato, kafin a tare ta a kusa da gefen garin Mangu.

Rahotanni sun bayyana cewa fasinjojin na kan hanyarsu ce domin halartar wani bikin aure kafin harin ya faru.

“Yayinda motar ke tsallaka duhun titunan Filato da misalin ƙarfe 9:47 na dare, sai ga wasu matasa daga cikin al’umma sun tare ta a wajen da ba nisa da gari ba. Abin da ya biyo baya kuwa ya kasance tashin hankali da rikici mai ban tsoro,” in ji Makama.

Nan take mutum bakwai suka mutu a wurin harin. Wani fasinja ya jikkata sosai, yayin da mutane shida suka samu raunika daban-daban. Bayan haka, maharan sun kona motar gaba ɗaya, sannan suka bar gawarta tana ƙonewa a matsayin abin tunawa da mummunan harin.

A cikin rikicin, shugabannin al’umma sun hanzarta shiga tsakani, inda suka ceto mutane 14 da suka tsira ba tare da wani rauni ba. Wannan ɗaukar matakin cikin gaggawa ya taimaka wajen kare karin rayuka daga salwanta.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an tura tawagogin sintiri zuwa yankin domin dakile yuwuwar wani sabon hari. Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wani bayani da jami’an ‘yan sanda ko na rundunar soja suka fitar a hukumance dangane da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here