Gidaje 62 sun ƙone sakamakon rikicin makiyaya da manoma a jihar Taraba

0
26

Mutum ɗaya ya jikkata, yayin da gidaje 62 suka ƙone sakamakon rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba.

Rahoton da Channels TV ta bayar ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga takaddama kan amfani da wani tafki da ke tsakanin garuruwan Tor Bali da Atongo a cikin ƙaramar hukumar.

Shugaban ƙaramar hukumar Bali, Aboki Dauda, ya bayyana cewa rikicin ya fara bayan da wasu makiyaya suka kai hari kan wata mata da ke debo ruwa a tafkin, inda suka kawo shanunsu su sha ruwa.

Dauda ya ce rikicin ya ƙara tsananta bayan matar ta riƙa yin ihun neman agaji, inda al’umma suka fito domin taimaka mata.

“Abin da ya faru yana da muni ƙwarai. Gidaje sun ƙone, mutane sun rasa matsuguni, amma muna gode wa Allah babu rai da aka rasa,” in ji Dauda.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce sun kira shugabannin makiyaya, sun kuma ja kunnensu game da illar faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

Gwamnatin jihar Taraba ta bayyana rashin jin daɗinta kan faruwar lamarin, inda ta ce ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya a jihar ba.

Wata tawaga ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ayyuka na musamman da walwalar jin ƙai, Saviour Noku, ta kai ziyara ga al’ummomin da abin ya shafa, inda suka raba kayan tallafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here