Jagoran Ƙoli na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya zabi jerin mutane uku da za su iya maye gurbinsa, idan har aka kashe shi ta hanyar kai hari daga Amurka, Isra’ila ko kuma wakilansu.
Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa, saboda yiwuwar kai masa hari, Ayatollah Khamenei yanzu ya takaita yin mu’amala kai tsaye da manyan kwamandojinsa sai ta hannun wani amintaccen hadimi, tare da dakatar da amfani da na’urorin sadarwar zamani domin rage yiwuwar gano inda yake.
Wani rahoto daga wasu manyan jami’an Iran sun tabbatar da wannan ci gaban ga manema labarai.
Ana zargin cewa Ayatollah Khamenei yana zaune a wata mafaka, inda ya tsara jerin wadanda za su iya gadar shi a cikin rundunonin soja idan har wasu daga cikin kwamandojinsa masu muhimmanci suka rasa rayukansu.
Ayatollah Khamenei, wanda yanzu ya kai shekaru 86, ya san cewa Isra’ila ko Amurka na iya yunkurin kashe shi kuma a cewarsa, hakan zai zama shahada gare shi, in ji jami’an.