Yan sanda sun kama ɗaruruwan masu laifi a Kaduna

0
27

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta sanar da kama mutane 398 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a wani gagarumin samame da aka kaddamar domin dakile ayyukan laifi a fadin jihar.

Wannan samame dai an gudanar da shi cikin kwanaki tara, ƙarƙashin wata rundunar haɗin gwiwa ta musamman da gwamnatin jihar ta kafa, inda rundunar ‘yan sanda ke jan ragamar aikin.

Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 18 ga Yuni. Ya ce samamen ya samo asali daga sahihan bayanan sirri da suka taimaka wajen kama wadanda ake zargi a sassa daban-daban na jihar.

Daga cikin wadanda aka kama akwai wani shahararren jagoran ‘yan daba mai suna Mathew Adamu, inda aka kama shi da bindiga a hannunsa. Haka zalika, an cafke wani mashahurin mai safarar miyagun ƙwayoyi mai suna Adamu Umar, wanda aka ce za a mika shi ga hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.

Rundunar ta kuma samu nasarar kwato makamai masu haɗari, miyagun ƙwayoyi da kuma wayoyin salula guda 29 da aka sace.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Rabiu Muhammad, ya bukaci rundunar ta musamman da su ci gaba da zage damtse don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here