Yakin mu da Iran zai iya ɗaukar lokaci mai tsawo—Isra’ila

0
35

Yakin da Isra’ila ke yi da Iran, wanda yanzu ya shiga mako na biyu, zai iya ɗaukar lokaci mai tsawo, in ji shugaban rundunar sojin ƙasar, Eyal Zamir, yayin da ƙasashen biyu ke cigaba da musayar hare-hare, sannan ƙasashen Turai na kokarin cimma matsaya ta diflomasiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

“Dole mu kasance cikin shiri domin yaƙi mai tsawo,” in ji Zamir cikin wata sanarwar bidiyo da aka haskawa ‘yan Isra’ila, kwanaki takwas bayan ƙasar ta kaddamar da jerin hare-hare da ta ce manufarsu ita ce dakile burin Iran na kera makaman nukiliya.

“Mun shiga cikin daya daga cikin mafi wahalar yakin da muka taɓa fuskanta don kawar da barazana mai girma,” in ji shi.

“Ba mu kammala ba. Duk da nasarorin da muka samu, har yanzu muna fuskantar kalubale masu nauyi.”

Iran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da jiragen drone, inda hukumomin Isra’ila suka ce mutane akalla 25 sun mutu.

Wani asibiti da ke tashar jiragen ruwa ta Haifa a Isra’ila ya ce ya karɓi mutane 19 da suka jikkata, ciki har da wanda ke cikin mawuyacin hali, sakamakon wani harin Iran da Shugaban Ƙasa Isaac Herzog ya ce ya kai har da wani masallaci.

Iran ta bayyana a ranar Lahadi cewa hare-haren Isra’ila tun daga ranar 13 ga Yuni sun hallaka akalla mutane 224, ciki har da kwamandojin soji, masana nukiliya da fararen hula.

Yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke nazari kan yiwuwar shiga cikin wannan rikici, manyan jami’an diflomasiyya daga Birtaniya, Faransa da Jamus sun gana da wakilin Iran, Abbas Araghchi, a ranar Juma’a.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasashen Turai na kokarin gabatar da mafita ta diflomasiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here