Sai bayan babban taron APC Tinubu zai fitar da mataimakin sa a zaɓen 2027—Fadar shugaban ƙasa

0
26

Sai bayan babban taron APC Tinubu zai fitar da mataimakin sa a zaɓen 2027—Fadar shugaban ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa ba za a zaɓi wanda zai rike matsayin mataimakin shugaban ƙasa Tinubu a zaɓen 2027 ba  har sai bayan babban taron jam’iyyar APC.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.

A ‘yan kwanakin nan dai, rahotanni sun nuna alamun rashin jituwa a cikin jam’iyyar APC dangane da batun wanda zai yiwa Tinubu mataimaki a zaɓe mai zuwa, musamman bayan da gwamnonin jam’iyyar suka nuna goyon baya ga Tinubu a matsayin ɗan takarar APC a 2027, ba tare da bayyana goyon bayan Kashim Shettima ba.

A wani taro da aka gudanar a ƙarshen mako tsakanin shugabannin jam’iyyar daga shiyyar Arewa maso Gabas, rikici ya kusa ɓarkewa bayan da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka soki yadda aka gaza ambaton sunan mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a lokacin da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje, yayi jawaban amincewa da takarar Tinubu a zaɓe mai zuwa, ba tare da Kashim Shettima ba.

Tun daga lokacin dai, babu wani martani daga fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya haifar da jita-jitar cewa ana shirin canza Kashim Shettima daga tikitin takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Sai dai Bayo Onanuga ya karyata hakan, yana mai cewa lokaci bai yi ba na ayyana wanda zai zama mataimakin shugaban ƙasa a shekarar 2027.

A tsarin takarar shugaban ƙasa, ana fara tsayar da ɗan takara, daga baya kuma a zaɓi mataimakinsa. Haka aka yi lokacin Buhari, an fara da shi, daga baya ne aka bayyana mataimakinsa. Ba a yin hakan lokaci guda, in ji Onanuga.

Wasu na ganin cewa Tinubu zai iya canza mataimakinsa, la’akari da yadda ya yi lokacin da yake gwamnan Legas, inda ya sauya mataimaki fiye da sau ɗaya.

Amma Onanuga ya ce wannan hasashe ne kawai.

Eh, lokacin yana gwamna akwai wasu dalilai. A wa’adin farko ba su jitu da mataimakiyarsa Kofo ba, hakan ya sa ta ajiye aikinta. Femi Pedro ne ya gaje ta. A wa’adi na biyu, ya ci gaba da aiki da Pedro, sai daga baya Pedro ya sauya sheƙa saboda yana son ya tsaya takarar gwamna, shi ya sa aka rabu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, don haka ba daidai ba ne a ce Tinubu yana da ɗabi’ar canza mataimakinsa. Wannan tunanin mutane ne kawai.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here