Matatar Dangote ta ƙara farashin litar man fetur 

0
27

Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara farashin litar man fetur zuwa naira 880, daga tsohon farashin naira 825.

Wannan sauyin farashi, wanda aka tabbatar da shi a ranar Juma’a, ya ƙara haifar da fargaba game da saukin samun daidaiton farashin man.

Hakan ya nuna cewa an samu karin Naira 45 akan tsohon farashin

Ana sa ran wannan karin farashin zai shafi dukkan harkar rabon man fetur, wanda zai iya janyo lita ɗaya ta kai fiye da naira 900 musamman a yankunan da ke nesa da matatar Dangote.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here