Kotu ta samu hannun Nnamdi Kanu a zanga-zangar EndSARS

0
22

Kotu ta samu hannun Nnamdi Kanu a zanga-zangar EndSARS

Kotu Ta Amince da Rahoton DSS da ke Danganta Nnamdi Kanu da Kisan ‘Yan Sanda 186 da Lalata Ofisoshi 164 Lokacin Zanga-zangar #EndSARS

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin Abuja ta amince da gabatar da wani rahoto daga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) wanda ake zargin yana da alaƙa da jagoran ƙungiyar (IPOB), Nnamdi Kanu, kan kisan ‘yan sanda 186 da rushe ofisoshin ‘yan sanda 164 a lokacin zanga-zangar EndSARS.

Mai shari’a James Omotoso ne ya amince da shigar da rahoton a matsayin hujja yayin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa Kanu bisa zargin ta’addanci a ranar Alhamis.

Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Adegboyega Awomolo (SAN), ne ya gabatar da rahoton ta bakin wani jami’in DSS da aka bayyana da sunan sirri “Mr EEE” saboda dalilai na tsaro, a matsayin shaida na biyar.

Yayin da yake ba da shaida a gaban kotu, Mr EEE ya ce shi da wasu jami’an DSS an tura su zuwa yankin Kudu maso Gabas da wasu sassa na ƙasar nan domin tattara bayanai da rubuta rahotanni game da tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar EndSARS.

“Na san wanda ake zargi ne ta kafafen yaɗa labarai, amma ban taɓa haɗuwa da shi kai tsaye ba,” in ji shaidan.

EEE ya ƙara da cewa aikinsa shi ne tattara bayanai kan lalata dukiyoyin gwamnati da kashe jami’an tsaro, waɗanda ake zargin sakamakon kalaman Kanu ne suka faru.

Kotu ta karɓi wasu hujjoji da suka haɗa da rahoton kimanta asara, takardun mutuwar wasu jami’an tsaro, da kuma takardar bin ƙa’ida da lauyan gwamnati ya gabatar ta bakin shaida.

Mai shari’a Omotoso ya dage cigaban sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga Yuli domin gabatar da ƙarar “babu laifi”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here