Dubban mutane ne suka hallara a babban birnin Iran, Tehran, bayan sallar Juma’a domin gudanar da zanga-zangar adawa da Isra’ila, kamar yadda hotunan talabijin na gwamnati suka nuna. Masu zanga-zangar na ɗaga taken goyon baya ga shugabanninsu tare da ɗaga kwalaye da hotunan kyamar Yahudawa.
“Juma’ar hadin kan al’ummar Iran ce a yau, da kuma nuna juriya a fadin kasar,” in ji mai gabatar da labarai na gidan talabijin na gwamnatin Iran.
Bidiyon da aka nuna ya bayyana wasu masu zanga-zangar suna rike da hotunan kwamandojin da suka rasa rayukansu tun bayan barkewar rikici da Isra’ila, yayin da wasu ke daga tutocin Iran da na kungiyar Hezbollah ta Lebanon.
Gidan talabijin na Iran ya kara da cewa an gudanar da makamanciyar wannan zanga-zanga a wasu manyan birane na kasar, ciki har da Tabriz da ke arewa maso yammacin Iran da Shiraz a kudu.