Hadakar ƴan siyasar dake son ƙalubalantar shugaban ƙasa Tinubu a zaɓen shekarar 2027 (NNCG), ta nemi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ta yi mata rajistar sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna All Democratic Alliance (ADA).
Takardar buƙatar, rijistar jam’iyyar wadda aka aike ranar 19 ga Yuni 2025, ta samu amsa daga INEC a ranar 20 ga Yuni.
Chief Akin A. Rickets, Shugaban Riko na haɗakar ne ya sanya wa takardar hannu.
Cikin manyan jiga-jigan da ke da alaƙa da NNCG akwai Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai, da Dr. Umar Ardo. Bayan gazawar haɗewa da jam’iyyun ADC da SDP, NNCG ta yanke shawarar kafa sabuwar jam’iyya mai zaman kanta domin tabbatar da daidaito da karɓuwa tsakanin mambobinta.