
Fararen hula ne ke bawa ƴan ta’addan Benue bayanai akan sojoji—Christopher Musa
Shugaban Hafsoshin Tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, ya ce sojojin Najeriya sun samu bayanan karya daga fararen hula kafin harin kisan gillar da ya faru a jihar Benue.
Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis, Janar Musa ya bayyana cewa a ranar da harin ya faru, an shaida wa sojoji da ke garin Yelewata cewa wani kauye daban yana fama da hari.
Ya ce sojojin da ke Yelewata sun nufi kauyen da aka ce an kai masa hari, sai kuma masu kai harin suka kutsa Yelewata suka kashe jama’a.
Shugaban tsaron ya zargi wasu mazauna yankin da bayar da bayanai ga ‘yan ta’adda dangane da motsin dakarun soji.
“A ranar da harin ya auku, sojoji suna cikin garin,” in ji shi. “An basu bayanan karya cewa ana kai hari a wani kauye daban, sai suka tafi can, daga nan ne aka kai harin a Yelewata. Wannan shi ne abin da ya faru.”
“Wasu daga cikin mutanen yankin ne ke bawa mahara bayanai game da motsin dakarun. Ina tabbatar muku cewa yayin da sojoji ke tafiya zuwa wani aiki, akwai mutanen da ke bibiyar su.”
“Wasu na sanar da su yawan motocin da sojojin da ke tafe. Ana basu duk wadannan bayanai.”
A ranar 14 ga Yuni, wasu ‘yan bindiga sun kai mummunan hari kan al’ummomin Yelewata da Daudu da ke karamar hukumar Guma a jihar Benue, inda aka kashe fiye da mutane 200.
Wannan kisan gillar ya tayar da kura a fadin kasar, lamarin da ya sa Shugaba Bola Tinubu yin ziyarar gaggawa zuwa jihar Benue a ranar 18 ga Yuni.