Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ƙarƙashin atisayen Operation Hadin Kai, ta lalata wani wurin kera na’urorin fashewa (bama-bamai), da lalata motocin yaƙi na ‘yan ta’adda, tare da kashe daruruwan mayaƙa a Kwaltiri, cikin yankin Tumbuktu Triangle na jihar Borno.
Wannan jawabi na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da jama’a na rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja.
Ejodame ya bayyana cewa hare-haren saman da aka kai a ranar Laraba sun biyo bayan rahotannin sirri da suka nuna ayyukan ‘yan ta’adda a yankin.
Ya ce binciken da jiragen leƙen asiri suka yi ya tabbatar da akwai wurin kera bama-bamai da kuma wasu motoci a wurin, wanda jiragen yakin suka kai musu hari.
A cewar sa, wannan aiki ya kasance babbar illa ga ƙarfin mayaƙan, domin hare-haren sun tarwatsa tsarin jagoranci da hanyoyin jigilar kayayyaki na ‘yan ta’addan, tare da haifar da ruɗani a tsakanin su, lamarin da ya rage musu ƙwarin guiwa da kuzarin gudanar da hare-hare.
“Wannan aiki ya ƙara tabbatar da aniyar NAF na ci gaba da rage ƙarfin ‘yan ta’adda da inganta tsaro a yankin Arewa maso Gabas,” in ji shi.