Sanata Natasha ta gurfana a gaban kotun tarayya

0
20

Dakatacciyar Sanata mai wakiltar Mazabar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan, ta isa Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Maitama, Abuja, domin gurfana a gaban kuliya kan zargin bata suna.

Sanata Akpoti-Uduaghan ta shiga cikin kotu da misalin ƙarfe 10:30 na safe, kafin zaman kotu da aka shirya farawa da ƙarfe 11:00, inda ake jiran zuwan alkalin da zai jagoranci sauraren shari’ar.

Babban Daraktan Ɗaukar Nauyin Gurfanar da Masu Laifi na Ƙasa, Mohammed Abubakar, ne ya shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya a kan Sanata Akpoti-Uduaghan.

A cikin ƙarar mai lamba CR/297/25, Gwamnatin Tarayya ta zargi Sanatar da yin maganganu masu cin mutunci da suka shafi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a wani shirin talabijin da aka watsa kai tsaye.

Sanarwar ƙarar ta bayyana Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin masu kai ƙorafi a shari’ar.

An zargi Sanatar da cewa ta bayyana a fili cewa Yahaya Bello ya haÉ—a baki da Akpabio domin shirya mata kisan kai a wajen birnin Abuja.

Gwamnatin Tarayya ta ce Sanatar ta yi wannan zargi ne a wani shirin Politics Today na talabijin yChannels  a ranar 3 ga Afrilu, 2025.

A cewar Gwamnatin Tarayya, Sanatar ta yi waɗannan kalamai ne da gangan ko da rashin kulawa, tare da sanin cewa hakan zai iya ɓata suna da mutuncin waɗanda abin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here