A yau Alhamis ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyarar aiki ta yini ɗaya a Jihar Kaduna, inda ya kaddamar da jerin muhimman ayyukan ci gaba da aka samar domin inganta ababen more rayuwa da hidimomin jama’a a jihar.
Shugaban ya iso sansanin rundunar sojin saman Najeriya da ke Kaduna, inda Gwamna Uba Sani tare da manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da sauran manyan baki suka tarbe shi cikin girmamawa.
Bayan isowarsa, Shugaba Tinubu ya wuce Rigachikun da ke ƙaramar hukumar Igabi, inda ya bude wasu muhimman ayyuka da suka haɗa da sabbin hanyoyin mota, cibiyoyin kiwon lafiya da aka gyara, da kuma sabbin gine-ginen makarantu na zamani, dukkansu cikin shirin ƙara bunƙasa tattalin arziki da walwalar al’umma a jihar.
Wadannan ayyuka na cikin shirin gwamnatin Jihar Kaduna na ƙarfafa ci gaban karkara da inganta samun saukin shiga ayyukan more rayuwa ga jama’a.
An tsaurara matakan tsaro a muhimman sassan birnin Kaduna yayin ziyarar, inda jami’an ‘yan sanda, NSCDC, da na sojoji suka hada kai wajen tabbatar da tsaro.