Mahara sun kashe manoma a jihar Katsina

0
22

Akalla manoma 20 ne suka rasa rayukansu, tare da wasu mutane uku da wani jami’in sa kai na C’watch, a hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a yankin Karamar Hukumar Kankara da ke jihar Katsina.

Wannan lamari ya faru ne a sassa daban-daban na Karamar Hukumar Kankara, wacce take daya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro a jihar.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa kwanaki shida da suka wuce, ‘yan bindiga sun kai farmaki kan manoma a kauyukan Yargoje, Kwakware, Danmarke, Gidan Dawa da kuma wasu daga Burdugau. Sun kashe akalla manoma 20, sun yi garkuwa da wasu, sannan suka kwashe dabbobin da ake amfani da su wajen noman.

Wata majiyar daban ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa a ranar Litinin, ‘yan bindiga sun kuma kai hari a kauyen Marmara da ke cikin Karamar Hukumar Kankara, inda suka yi arangama da jami’an C’watch da kuma mambobin sa-kai na Civilian JTF. A yayin arangamar, sun kashe wani dan sa-kai na C’watch, tare da jikkata wasu biyu daga Civilian JTF a wajen kauyen.

A wani ci gaba kuma, rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta sanar da cewa ta dakile wani yunƙurin sace mutane a kauyen Mazare da ke Karamar Hukumar Sabuwa, inda ta ceto mutane hudu da suka hada da mata uku da wata jaririya.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, lamarin ya faru ne a ranar 18 ga Yuni, da misalin ƙarfe 9 na dare, inda aka samu rahoton harin da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai kauyen, kuma suka harbi mutane biyu tare da ƙoƙarin yin garkuwa da wasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here