Kotu ta bayar da belin Natasha akan Naira miliyan 50

0
22

Wata babbar kotun tarayya dake Maitama, Abuja ta bayar da belin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, akan kudi Naira miliyan 50, bayan da gwamnatin tarayya ta gurfanar da ita kan zargin ɓata suna.

Mai shari’a Chizoba Orji, wacce ke jagorantar sauraron shari’ar, ce ta yanke wannan hukuncin a ranar Alhamis, inda ta yi watsi da bukatar da lauyoyin gwamnati suka gabatar ta neman a tsare sanatar a gidan gyaran hali.

A cewar mai shari’a Orji, kotu ba ta ga wani kwararan dalili da zai sa a hana Natasha beli ba, tana mai cewa akwai isassun hujjoji da ke nuna cewa tana da niyyar fuskantar shari’ar da ake yi mata.

Kotun ta kuma gindaya sharadi cewa dole ne Sanatar ta gabatar da mutum guda da zai tsaya mata, wanda zai kasance mutum nagari, mai kima a idon al’umma, tare da mallakar kadarar fili ko gida a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here