Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta lamunci ci gaba da rayuwar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ba, yana mai cewa dole ne ya ɗauki alhakin hare-haren da suka faru.
Katz ya yi wannan barazana ne bisa zargin cewa Iran ce ke da alhakin harin makami mai linzami da aka kai wani asibiti da ke kusa da birnin Tel Aviv. Rahotanni sun ce an ƙoƙarta kwashe marasa lafiya daga cibiyar lafiyar kafin harin domin ceto rayukansu.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya kai ziyara zuwa Cibiyar Lafiya ta Soroka da ke Beersheba — ɗaya daga cikin wuraren da harin ya shafa.
Sai dai Iran ta musanta kai harin asibiti, tana mai cewa hare-haren nata sun nufi sansanin sojoji ne da ke kusa da wurin, ba cibiyar lafiya ba.
Kalaman Israel Katz sun zo ne bayan kashe wasu manyan kwamandojin Iran, kuma sun nuna yiwuwar Isra’ila za ta kai hari kai tsaye kan Ayatollah Khamenei.