Sojoji sun dakile harin Boko Haram a sansanin sojojin ruwa

0
69

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta na Operation Hadin Kai sun dakile wani yunkurin kai hari da mayaƙan Boko Haram da ISWAP suka yi a sansanin sojojin ruwa da ke kusa da Tafkin Chadi, a yankin Fish Dam, inda suka kashe da dama daga cikin mayakan a wani samame na haɗin gwiwa.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na dare, inda ‘yan ta’addan suka zo da nufin lalata sabbin motocin ruwa da gwamnatin Jihar Borno ta tanada domin share hanyoyin ruwa a yankin.

Sai dai, rundunar ta ce ƙoƙarin ‘yan ta’addan ya ci tura, bayan da sojojin ruwa a sansanin suka yi musu kwanton ɓauna tare da samun ƙarin goyon bayan dakarun sojin kasa daga sansanin Baga.

“An yi musayar ɓarin wuta mai tsanani na tsawon sama da sa’o’i biyu wanda a ƙarshe ya tilasta musu janyewa ba tare da cimma manufarsu ba. Dakarunmu sun kashe da dama daga cikinsu tare da kwato wasu makamai da abubuwan hada bam,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa duk da haka, mayakan sun lalata wasu kayayyakin aiki guda uku, ciki har da motar daukar marasa lafiya da wasu motocin aiki biyu. Rundunar ta kuma tabbatar da cewa wasu daga cikin dakarunta sun samu raunuka a yayin musayar wutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here