Rundunar ƴan sandan Gombe ta hana hawa babur saboda masu ƙwacen waya
Wasu mazauna Jihar Gombe sun nuna rashin jin daɗinsu kan sabon umarnin da Rundunar ‘Yan Sandan jihar ta bayar, na takaita amfani da babura daga ƙarfe 7 na dare zuwa 6 na safe a fadin jihar.
A ranar Laraba ne Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Gombe ta sanar da haramta amfani da babura ɗin a wani yunkuri na dakile ƙwacen wayoyi da kuma sauran laifuka da ke yawan faruwa a jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa rundunar ta kuma hana daukar makamai masu haɗari a wuraren taruka yayin bukukuwa, al’amuran siyasa, da sauran su.
Ya kara da cewa an haramta daukar fiye da mutum daya a babur.
“Aikin da muke yi na cikin matakan tsaro da muka dauka tun da wuri, don hana tashin hankali, razana jama’a, da kuma faruwar abubuwan da za a iya kauce wa, wadanda ke yawan faruwa sakamakon amfani da makamai kamar wuƙaƙe, adduna, takubba, sanduna da makamantansu a wuraren taruka,” in ji shi.
DSP Abdullahi ya ce rundunar ba za ta lamunci wani abu da zai tada hankalin jama’a ba, musamman idan an boye shi da sunan biki, rigimar unguwanni ko na kungiyoyi.
Sai dai wasu daga cikin mazauna jihar sun bayyana cewa wannan dokar ta yi tsauri matuƙa.
A nasa bangaren, Nasir Isah Bello na ƙungiyar masu kishin al’ummar Gombe ya buƙaci rundunar ta sake duba dokar, inda ya ba da shawarar a ɗaga lokacin daga ƙarfe 7 zuwa 9 na dare. A cewarsa, “’Yan daba masu satar waya, musamman ‘yan Kalare, ba lallai ne su riƙa hawa babura yayin aikata laifi ba.”