Rikicin Isra’ila da Iran ka’iya haifar da tsadar fetur a Najeriya—Masana

0
149
man fetur
man fetur

Masana sun bayyana damuwa kan rikicin da ke gudana tsakanin Isra’ila da Iran, inda suka ce lamarin ka iya haddasa tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, wanda hakan zai iya haifar da matsin lamba a tattalin arzikin yan Najeriya.

Cibiyar Commercio Partners da ke Legas ce ta bayyana hakan a cikin wani rahoto da ta fitar, mai taken: “Farashin kayayyaki ya sauka a Najeriya a watan Mayu, amma akwai matsala a nan gaba”, wanda aka wallafa a ranar 16 ga Yunin 2025.

A cewar rahoton, rikicin da ke ci gaba da kazanta a yankin Gabas ta Tsakiya na iya rage yawan man fetur da ake fitarwa a duniya, wanda hakan zai kara matsin lamba ga farashin sa a kasuwannin kasa da kasa.

Ko da yake Najeriya kasa ce mai arzikin danyen mai, masana sun nuna cewa tashin farashin ba lallai ne ya haifar da alheri ga tattalin arzikin kasar ba.

A yanzu  farashin danyen mai ya haura Dala 75 kan kowacce ganga a ‘yan kwanakin baya, wanda ke nuni da yiwuwar ci gaba da hauhawar farashi.

Sai dai wannan hauhawar farashin na iya janyo karin wahala ga ‘yan Najeriya, inda ake hasashen farashin lita guda na man fetur zai iya kaiwa har Naira 1,000, idan aka ci gaba da tafiya a haka.

Yanzu haka ana sayar da man fetur tsakanin N870 zuwa N920 a gidajen mai.

Masanan sun kara da cewa tun da aka janye tallafin man fetur a Najeriya, farashinsa ya ta’allaka da canje-canjen da ke faruwa a kasuwannin duniya. Don haka duk wani tashin farashi a waje na da tasiri kai tsaye a gida.

Sun ce idan farashin danyen mai ya kara tashi, zai yi wuya a kauce wa hauhawar farashin litar man fetur a cikin gida zuwa akalla Naira 1,000, lamarin da zai kara wa ‘yan kasa ƙunci.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here