Gwamnatin tarayya zata kwaso yan Najeriya daga ƙasashen Iran da Isra’ila

0
73

Gwamnatin tarayya zata kwaso yan Najeriya daga ƙasashen Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa tana kan hanyar kammala shirye-shiryen gaggawa domin kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a ƙasashen Isra’ila da Iran, sakamakon ƙara tsananta rikici tsakanin ƙasashen biyu.

Wannan jawabi na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a daren Talata, inda ya tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Najeriya da ke biranen Tel Aviv da Tehran suna aiki kafada da kafada da ‘yan Najeriya da rikicin ya shafa domin tabbatar da tsaron lafiyarsu da kuma ceto su cikin gaggawa.

Ma’aikatar ta bukaci dukkan ‘yan Najeriya da ke cikin waɗannan ƙasashe biyu da su bi umarnin hukumomin tsaro na ƙasashen da suke ciki, tare da gaggauta tuntubar ofishin jakadancin Najeriya mafi kusa domin yin rajista da samun karin bayani.

Haka kuma, Ma’aikatar Harkokin Waje ta yabawa ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Najeriya a Isra’ila da Iran ke yi, tare da jaddada cewa kare lafiyar ‘yan Najeriya da ke ƙetare na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin tarayya ke bai wa muhimmanci.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa ganin yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, gwamnatin tarayya na ƙoƙarin kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba domin tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya da za a barshi a cikin haɗari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here