Wani ce-ce-ku-ce ya taso a fadin Najeriya bayan bayyana wani bidiyo da ke nuna yadda ake bukatar caje ƴan mata ɗalibai kafin su shiga ɗakin jarrabawa, tare da duba rigar maman su.
A bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an hango wasu malaman Jami’ar Olabisi Onabanjo da ke jihar Ogun suna duba rigar mama ta wasu ɗalibai mata yayin da suke cikin layin shiga ɗakin rubuta jarrabawa.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’ar na da wata doka da ke buƙatar kowace ɗaliba ta sanya rigar mama kafin ta shiga ɗakin jarrabawa, bisa wani tsarin da ake dangantawa da dokokin kamun kai na jami’ar.
Sai dai hakan ya haifar da martani kala-kala daga al’umma, inda masu suka ke ganin wannan doka ta daɗe kuma tana da alamar ƙarfafa cin zarafin mata da kuma haifar da rashin jin daɗi ga ɗalibai. Wasu na ganin hakan wani nau’in cin zarafin lalata ne da ya saba da tarbiyya da kuma ‘yancin ɗalibai mata.