Jagoran addinin kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi gargaɗi cewa Iran za ta dauki matakin ramuwar gayya cikin tsanani idan Amurka ta yi yunkurin kai mata hari da karfin soji.
A cikin wata sanarwa da ya fitar wacce aka karanta ta a gidan talabijin na ƙasar, Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa Iran ba za ta zura ido tana kallon hare-hare daga Amurka ba tare da martani ba.
“Idan Amurka ta kuskura ta yi amfani da karfin soja, to za ta gamu da lahani mai tsanani wanda ba za a iya gyarawa ba,” in ji shi.
Jagoran ya ƙara da cewa duk wanda ke da fahimta da ilimi game da Iran da al’ummarta da kuma tarihin ta, ba zai kuskura ya yi mata barazana ba, domin Iraniyawa mutane ne masu kishin ƙasa waɗanda ba sa miƙa wuya cikin sauƙi.