Wani mutum da aka bayyana sunansa da Suleiman Muntari, ɗan asalin Jihar Neja kuma mazaunin Kofar Gadon Kaya a Kano, ya ƙone kansa da wuta da safiyar yau a unguwar Diga, kan titin Panshekara.
Rahotonni sun bayyana cewa Suleiman ya zuba fetur a jikinsa kafin ya kunna wuta da kansa.
“Ya ce yana so ya je Aljanna,” in ji Saminu Isah, wani mai gyaran taya da ke kusa da inda lamarin ya faru. “Mutane sun ɗauka wasa yake yi, kafin a kai masa ɗauki har ya zuba fetur a jikinsa ya kunna wuta. Cikin ƴan daƙiƙu, wuta ta kama shi.”
Wata mazauniyar unguwar mai suna Aisha Salisu ta ce alamu sun nuna cewa mutumin baya cikin hayyacinsa lokacin da lamarin ya faru.
“Baya cikin natsuwarsa kwata-kwata, sannan za ka iya jin ƙamshin wani abu mai ƙarfi a jikinsa, yana rawa kuma yana faɗin abubuwan da ba a gane ba,” in ji ta. “Mutane sun firgita, wasu sun gudu, wasu kuma sun ƙoƙarta su zuba masa ruwa, amma abin ya riga yaci tura.
Wasu matasa daga unguwar sun yi ƙoƙarin ceto shi ta hanyar jan shi zuwa ramin ruwa da ke gefen titi, amma wutar ta riga ta yi mummunan barna a jikinsa.
“Abin yayi muni,” in ji Ibrahim Jafar, wani mai tuka babur mai kafa uku. “Wasu matasa sun ƙwace shi suka jefa shi cikin ruwan da ke cikin ramin, amma wutar ba ta mutu nan take ba. Fatar jikinsa har ta fara fita.”
Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba zuwa yanzu.