Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta fitar da gargaɗi mai ƙarfi kan masu nuna makamai a bainar jama’a da sunan gudanar da wasannin gargajiya irin su Kidan Gangi, biyo bayan cafke mutane 51 da ake zargi da hannu cikin ta’addanci a fadin birnin Kano.
A wata sanarwa da Mataimakin Jami’in hulɗa da Jama’a na ‘yan sandan Kano, DSP Hussaini Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samame na kwanaki uku daga ranar 13 zuwa 15 ga Yuni. An gudanar da atisayen ne domin tarwatsa maboyar miyagu, inda aka kai farmaki unguwanni da dama ciki har da Kofar Mata, Zage, Kurna, Rijiyar Lemo, Dorayi, Hotoro da Sheka a cikin ƙananan hukumomin Kano Municipal, Dala, Gwale da Tarauni.
A yayin samamen, an ƙwato makamai masu haɗari da miyagun ƙwayoyi, duk da cewa ba a fitar da cikakken bayani kan kayan da aka kama ba.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, yayin tsokaci game da lamarin, ya ja hankalin jama’a da kada su fake da al’adunsu wajen aikata tashin hankali. Ya nuna damuwa musamman kan Kidan Gangi wanda a wasu lokuta ake amfani da shi wajen nuna makamai da barazana ga zaman lafiya.
CP Bakori ya kuma nuna damuwa kan yadda matasa ke saka hotuna da bidiyon nuna makamai da al’amuran da suka shafi ‘yan daba a shafukan sada zumunta kamar TikTok, Facebook, Instagram da X, yana mai cewa hakan na ƙarfafa aikata laifi.
Rundunar ta kuma ja kunnen masu sana’ar ƙera makamai da kada su shiga irin wannan abu, inda ta ce za a bincike su tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.