Najeriya ce jagorar fitar da fetur a nahiyar Afirka—OPEC

0
83

Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta duniya, OPEC, ta bayyana cewa duk da raguwar adadin man da Najeriya ke fitarwa, har yanzu ita ce ƙasar da ta fi kowacce fitar da danyen mai a nahiyar Afirka.

A cikin rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin, OPEC ta ce fitar danyen mai daga Najeriya ya sauka zuwa ganga miliyan 1.45 a kullum a watan Mayu, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.48 da aka fitar a watan Afrilu.

Sai dai rahoton ya nuna cewa duk da wannan sauyi, Najeriya ta ci gaba da rike matsayinta na ƙasa mafi yawan fitar da danyen mai a Afirka, inda ta wuce ƙasashen Libya, Aljeriya da kuma Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

Har ila yau, rahoton ya ce wasu bayanai da suka fito daga hukumomin ƙasa sun nuna cewa Najeriya ta fitar da ganga miliyan 1.54 a kullum a watan Mayu wanda ya ɗan karu kadan daga ganga miliyan 1.52 da aka samu a watan da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here