Harin Iran ya dakatar da matatar mai ta Isra’ila

0
112

Hukumar da ke kula da matatar mai ta Isra’ila da ke yankin Haifa ta sanar da dakatar da dukkan ayyukanta, sakamakon harin da Iran ta kai wa matatar.

Kamfanin Bazan Group, wanda ke tafiyar da matatar, ya bayyana cewa harin da Iran ta kai ta hanyar amfani da makaman roka ya tilasta musu dakatar da aiki gaba ɗaya. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ke kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Bazan Group ya ce harin ya lalata tashar wutar lantarki da matatar ke dogara da ita. Baya ga haka, hukumomin Isra’ila sun tabbatar da mutuwar ma’aikata uku sakamakon harin.

Harin na Iran na cikin jerin hare-haren ramuwar gayya da ta ke kaiwa ta amfani da makamai masu linzami, bayan hare-haren jiragen yaki da Isra’ila ta kai a sassa daban-daban na Iran ciki har da birnin Tehran wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 220.

Rahotanni sun bayyana cewa kashi 70 cikin 100 na wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila mata da yara ƙanana ne, tare da wasu manyan jami’an tsaro da wani masanin kimiyyar makamashin nukiliya.

A baya-bayan nan, Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa hallaka jagoran addinin Iran, Ayatullah Ali Khamenei, na iya taimakawa wajen kawo ƙarshen rikicin.

Iran kuwa, a martaninta, ta yi gargadin cewa Isra’ila za ta fuskanci sakamako mai tsanani kan hare-haren da ta kai wa fararen hula, cibiyoyin soja da kuma tashoshin makamashin nukiliya a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here