Harin ƴan bindiga ya kashe jami’an tsaro da manoma a Katsina

0
94

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Marmara da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, inda suka kashe jami’ai hudu na rundunar tsaron a’lumma ta jihar da kuma wasu manoma da ba a san adadinsu ba.

Harin, wanda ya faru da yammacin Litinin, ya kuma bar wasu mutane da dama da jin rauni.

Wani masanin tsaro, Bakatsine, ya bayyana harin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata.

Yace a yammacin jiya, ‘yan bindiga sun kai hari kan manoma a wajen kauyen Marmara, dake Malumfashi.

Sai dai yace Gwamnatin Jihar Katsina na ci gaba da tattaunawa da wasu kungiyoyin ƴan bindiga a yankuna daban-daban domin cimma matsaya ta zaman lafiya.

Wasu kungiyoyi a kananan hukumomin Jibia, Batsari da Danmusa sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya tare da mika makamansu ga gwamnati.

Wannan sabon hari ya sake haifar da fargaba a zukatan al’umma dangane da dorewar kokarin samar da zaman lafiya a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here