Gwamnatin Jihar Benue ta sanar da Laraba, 18 ga Yuni, a matsayin ranar hutu ga ma’aikata.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Sakatariyar Gwamnatin Jiha, Deborah Aber, ta fitar a ranar Talata a birnin Makurdi.
An ayyana wannan hutu ne domin girmamawa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ake sa ran zai kai ziyara ta yini guda zuwa jihar.
Ziyarar na da nufin jajanta wa gwamnatin jihar da mazauna jihar kan matsalolin tsaro da suka addabi Benue a baya bayan nan.
Sai dai, ma’aikatan da ke gudanar da ayyuka irin na lafiya, jami’an tsaro da bankuna ba sa cikin waɗanda hutun ya shafa,” in ji sanarwar.
Aber ta kuma yi kira ga al’ummar jihar da su fito kwansu da kwarkwata domin tarbar Shugaban Ƙasa da tawagarsa.