‘Yan jam’iyyar APC a Jihar Adamawa sun bayyana goyon bayansu ga takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027, tare da nesanta kansu daga mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, yayin da suka nuna cikakken goyon baya ga mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Mallam Nuhu Ribadu.
A wani taro da aka gudanar a garin Hong ranar Talata, shugabannin jam’iyyar APC da manyan jiga-jiganta daga sassan jihar sun bayyana amincewarsu da shugabancin Tinubu.
Salihu Mustapha, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin Arewa maso Gabas, ya ce, manufar taron ita ce wayar da kai tsakanin shugabannin jam’iyya domin tabbatar da haɗin kai da ci gaban jam’iyya a jihar da ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa, Jam’iyyar karkashin jagorancin Tinubu ta samu nasarori masu yawa da suka haifar da gagarumin ci gaba a ƙasa.
Daga cikin nasarorin da ya lissafa sun haɗa da shirin sabon albashi na N70,000, biyan bashin albashi na baya, fafutikar samun ‘yancin kananan hukumomi, cire tallafin man fetur, da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.
Yusuf Captain-Buba, Shugaban Kwamitin Sulhu da Gyaran Jam’iyyar APC na Yankin Tsakiya ta Adamawa, ya ce Tinubu ya ɗauki matakai masu muhimmanci wajen farfaɗo da tattalin arziki da kuma sauya fannin noma.
Ya ce, tare da waɗannan nasarori da wasu da ba za mu iya lissafawa suna bayyana cikakken goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, bisa rawar da suke takawa wajen magance matsalar rashin tsaro da ke addabar sassan ƙasar nan.
Sai dai Buba bai ambaci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ba, sai dai ya jaddada cewa Mallam Ribadu yana da cikakken goyon bayan jiga-jigan APC na Adamawa.