Ƴan ta’adda sun ajiye mukaman su a jihar Katsina

0
147

Wasu manyan shugabannin ƴan bindiga da suka addabi ƙaramar hukumar Dan Musa a Jihar Katsina sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga hukumomi. Haka kuma, sun saki mutum 16 da suka hada da mata da yara da suke tsare da su.

Rundunar sojin Najeriya ce ta bayyana hakan a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X.

Sunayen fitattun jagororin da suka miƙa wuya sun haɗa da;

Kamulu Buzaru

Manore

Nagwaggo

Lalbi

Alhaji Sani

Dogo Baidu

Dogo Nahalle

Abdulkadir Black

A cewar wani rahoto, ƴan bindigar sun miƙa makamansu a ranar 14 ga Yuni, 2025, tare da alƙawarin daina aikata laifuka da zama lafiya da al’umma. Sojojin sun tabbatar da karɓar makaman, tare da miƙa su hannun hukumomi.

Don ƙara tabbatar da zaman lafiya, tsoffin ‘yan bindigar sun saki mata 7 da yara 9 da suka yi garkuwa da su, tare da alƙawarta sakin sauran da suke hannunsu.

Rundunar soji ta ce bayan wannan ci gaba, an samu kwanciyar hankali a yankin Dan Musa, kuma ana ci gaba da sanya ido domin hana sake ɓarkewar rikici.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here