Ɗaya daga cikin masana harkokin tsaro a jihar Kano, Detective Auwal Bala Durumin Iya, ya nemi lauyoyi su dena kare masu ƙwacen waya a gaban kotu a lokacin da aka gurfanar dasu.
Durumin Iya, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Daily News 24, akan kalubalen ƙwacen waya a jihar Kano, da hakan ke neman zama wata babbar musiba ga al’umma.
Ya kara da cewa maganar neman kawo karshen wannan matsalar abu ne da ya shafi kowa bisa hujjar cewa babu wanda yafi ƙarfin fadawa iftila’in ƙwacen waya.
Daga ɓangaren shari’a Durumin Iya, yace akwai bukatar kotuna su riƙe yanke hukunci mai tsauri akan duk wanda aka tabbatar ya aikata ƙwacen waya, tare da yin kira ga Alkalai su dena bayar da zaɓin biyan tara ga masu aikata laifin.
Babban dalilin da yasa ƙwacen waya ya yawaita a yanzu shine kusan kowa ya mallaki waya kuma ana saurin siyar da ita bayan ƙwacen, inji Durumin Iya.
Auwal Bala Durumin Iya, ya nemi a’lumma su ɗauki duk wasu matakan kare kai daga masu aikata wannan mummunar ɗabi’a.
Idan za’a iya tunawa a ƴan kwanakin nan ƙwacen waya yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a jihar Kano, musamman a cikin birni da kewaye.