Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana niyyarsa ta kai ziyara jihar Benue a ranar Laraba, domin jajanta wa al’ummar da harin da ake zargin wasu makiyaya sun kai.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin kaddamar da aikin faɗaɗa hanyoyin samar da ruwan sha na Abuja.
Ina mika ta’aziyya ga al’ummar jihar Benue, sannan na yi magana da gwamnan jihar, shugabanni da mutanen jihar domin su karɓi ta’aziyyarmu tare da ƙoƙarin ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsu, in ji Shugaba Tinubu.
Ya ƙara da cewa, “Na faɗa sau da dama cewa mu al’umma ɗaya ce, iyali ɗaya, muna zaune a gida guda koda yake a ɗakuna dabam-dabam muke.
Wannan bambancin namu ya kamata ya zama hanyar haɗin kai da ci gaba, ba tashin hankali ba, wanda dole ne mu riƙa sarrafa fushinmu da kuma ɓacin ranmu, inji shugaban.