Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa makiyaya dauke da makamai ne ke da alhakin hare-haren da suka sake kunno kai a jihar, inda ya ce makiyayan na shigowa jihar ba tare da shanu ba, sai dai manyan makamai irin su AK-47 da AK-49.
Gwamna Alia ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television, bayan wani hari da wasu mahara suka kai kauyen Yelwata da ke karamar hukumar Guma ta jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutane fiye da 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin.
Biyo bayan haka, matasan garin Yelwata sun toshe hanyar Lafia-Makurdi a matsayin boren nuna fushi da kashe-kashen.
Zanga-zangar ta cigaba da gudana har zuwa safiyar Lahadi a birnin Makurdi, inda ’yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar.
A cewar sa, bayan mahara sun kashe mutane da rusa garuruwa, wasu sabbin mutane kan shigo su mamaye yankunan da abin ya shafa.
Ya kara da cewa a shekarar data gabata mutane sun koma gidajensu suna noma, kuma sun samu albarkar amfanin gona mai yawa.