Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana kudirinsa na ganin an kawar da ayyukan ta’addanci da na ‘yan daba daga jihar, inda ya jaddada cewa babu wani wuri da zai kasance mafaka ga masu aikata laifuka da ke fakewa da sunan daba a Kano.
Wannan jawabi na ƙunshe cikin wata sanarwa da Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda, DSP Abdullahi Hussaini, ya fitar a madadin kwamishinan.
Sanarwar tazo bayan wani taron harkokin tsaro na musamman da aka gudanar a ranar 14 ga Yuni, 2025, da ya haɗa manyan kwamandoji, DPO da kuma shugabannin ƙungiyoyin dabarun aiki domin tsara sabbin hanyoyin yaki da ta’addancin ‘yan daba a cikin birnin Kano.
CP Bakori ya bai wa dukkan rundunonin da ke ƙarƙashin umarninsa cikakken izini su kaddamar da atisaye bisa leƙen asiri zuwa maboyar ‘yan daba. Ya gargadi cewa rundunar su ba za ta lamunci wani nau’in tashin hankali ko ƙungiyoyin masu tayar da zaune tsaye a tituna ba, yana mai cewa dole ne a dakile wannan barazana tun kafin ta mamaye al’umma.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa Kano za ta ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da tsaro, yana mai ƙarfafa guiwar al’umma su kwantar da hankula.
Domin cimma wannan manufa, rundunar za ta rungumi tsarin hulɗar jami’an tsaro da al’umma, ciki har da tattaunawa da shugabannin unguwanni da mazauna yankuna domin samun shawarwari da rahotanni kan hanyoyin inganta tsaro. Rundunar ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin tunkarar duk wani nau’in aikata laifi.
Daga ƙarshe, rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abu da suka zargi yana da alaka da laifi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta layukan gaggawa da rundunar ta tanada.