Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan bankin CBN akan zargin almundahana

0
110

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan babban bankin ƙasa (CBN), Godwin Emefiele, a gaban kotu kan zarge-zargen mallakar gidaje da dama a unguwar Lokogoma da ke birnin tarayya Abuja.

Emefiele ya bayyana a gaban Mai Shari’a Yusuf Halilu na Babbar Kotun tarayya dake Maitama, Abuja, inda aka gabatar masa da tuhuma guda takwas.

 Zarge-zargen sun shafi gidaje da aka ce sun kai 573, da ke filin lambobi 109, Cadastral Zone C09, a Lokogoma, wadanda ake zargin ya mallaka ba bisa ka’ida ba a lokacin da yake aiki.

An kuma tuhume shi tare da wani Eric Ocheme, wanda ake nema ruwa a jallo, a cikin shari’a mai lamba FCT/HC/CR/358/2025.

EFCC ta zargi Emefiele da mallakar biliyoyin naira a wasu asusun ajiya da ke bankin Zenith, da aka bude da sunan wasu mutane na daban domin boye ainihin masu asusun.

EFCC ta bayyana cewa laifukan sun sabawa tanade-tanaden Sashe na 319, 362 da 364 na Dokar Penal Code.

Sai dai Emefiele ya musanta aikata laifin a gaban kotu.

Lauyan masu kara, Rotimi Oyedepo (SAN), ya bukaci a sanya ranar fara shari’a domin gabatar da shaidun su a gaban kotu.

Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa (SAN), ya shaidawa kotu cewa sun riga sun mika bukatar neman beli ga kotu, kuma ya nemi a saurari wannan bukata, wanda Lauyan gwamnati bai yi wata gardama ba kan hakan ba.

Mai shari’a Halilu ya bayar da belin Emefiele kan kudi naira biliyan biyu tare da mutane biyu da za su tsaya masa, wadanda dole ne su kasance mazauna Abuja kuma sun mallaki fili ko gida a Maitama, Asokoro ko Wuse 2 dake Abuja.

Kotun ta bayar da umarnin cewa dole Emefiele ya cika sharuddan belin daga yau zuwa ranar Laraba, ko kuma a mayar da shi gidan yari.

Bayan haka an dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Yuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here