Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar Gwamnatin tarayya ta neman bayar da sammacin kama Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar yankin Kogi ta tsakiya kuma aka dakatar da ita, bayan ta gaza bayyana a gaban kotu domin gurfanar da ita kan tuhumar ɓatanci.
Mai shari’a Muhammed Umar ne ya yanke wannan hukunci, bayan da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya shaidawa kotu cewa an mika sammacin tuhumar ga lauyan Akpoti-Uduaghan a cikin zauren kotu da safiyar ranar Litinin ɗin nan.
Sai dai, Mai shari’a Umar ya bayyana cewa tunda ba a taba isar wa Sanatar da tuhumar ko takardar gayyata zuwa kotu ba, ba za a iya tsammanin ta bayyana ba.
Saboda haka, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar da lauyan gwamnati ya gabatar na bayar da sammacin kama ta.
Lauyan gwamnati ya kafe akan cewa lauyan Natasha ya samu takardar neman tazo kotu, don haka kamata ya yi ta san da shari’ar.
Amma Mai shari’a Umar ya ƙi amincewa da wannan hujja, yana mai cewa bai wadatar ba a doka a ɗauka cewa wadda ake tuhuma ta san da shari’ar idan kawai lauyanta ne aka miƙa wa tuhumar.
Tuhumar dai ta samo asali ne daga Babban Daraktan Gurfanar da Ƙara na Tarayya, Mohammed Abubakar, wanda ya shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya.
A cikin tuhumar, Gwamnati ta zargi Sanata Akpoti-Uduaghan da yin maganganu na ɓatanci yayin wata hira kai tsaye a talabijin.