Shugaban ƴan sandan ƙasa ya bayar da umurnin a kamo mai magana da yawun Gwamnan Kano akan zargin cin zarafin Ganduje

1
82

 Babban sufeton yan sandan ƙasa Kayode Egbetokun, ya umurci rundunar bincike ta kwamitin kula da ayyukan yan Sanda da ta kawo Sanusi Bature Dawakin-Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, zuwa Hedikwatar Ƴan Sanda ta kasa domin amsa tuhumar batanci da ake yi masa akan dakatar da shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar sa.

A shekarar 2024, kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC a mazabar Ganduje ya dakatar da Ganduje daga jam’iyyar, bisa zargin cin amanar jam’iyya da kuma rashin biyan kuɗin membobinsu.

An rawaito cewa Sanusi Bature ne ya jagoranci wannan dakatar da Ganduje, kasancewarsu ƴan ƙaramar hukumar ɗaya.

A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 23 ga Mayu, 2025, da lamba CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57, wacce aka aike wa Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Sufeto Janar ya buƙaci a saki Sanusi Bature Dawakin-Tofa domin bayyana a gaban SP Mojirode B. Obisiji a ranar Alhamis, 29 ga Mayu, 2025.

Wasiƙar da Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda, DCP Akin Fakorede, shugaban sashen binciken Sufeto Janar ne ya sa wa hannu, ta bayyana cewa:

“Rundunar Ƴan Sanda tana binciken zargin batanci ga mutum, cin fuska da gangan, keta sunu da kuma ɗabi’un da ka iya janyo tayar da hankali, wanda rahoton sa ya isa ofishin Sufeto Janar, kuma ake zargi shine mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano.”

“Dangane da haka, ana buƙatar ku bayar da Sanusi Bature Dawakin-Tofa domin ya bayyana domin amsa tambayoyi tare daga wajen SP Mojirode B. Obisiji, a ranar Alhamis, 29 ga Mayu, 2025, da karfe 12:00 na rana, a bene na farko, Louis Edet House, Hedikwatar Ƴan Sanda, Abuja, domin yayi ƙara bayani kan zargin da ake masa.”

Idan za’a iya tunawa a watan Disamba, 2024, Sufeto Janar ɗin ya bayar da umarni makamancin haka, inda ya tura jami’an bincike domin kama mai magana da yawun Gwamnan tare da kai shi zuwa Hedikwatar Bincike ta ƴan sanda a Abuja.


1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here